Ma'aikatan Gwamnati Na Yajin Aikin Kwana 10 A Guinea Bissau
Jul 25, 2018 06:35 UTC
A Guinea Bissau ma'aikata sun tsunduma wani yajin aiki na kwanaki goma, domin cilasta wa gawmnati yi masu karin albashi da kuma inganta yanayin aikinsu.
Babbar kungiyar kwadago ta kasar (UNTG), data kunshi mambobi ma'aikata 8,000 cikin 13,000 a fadin kasar ce ta kira yajin aikin na gama gari tun daga jiya Talata
Rahotanni sun ce yajin aikin ya samu karbuwa inda manyan ma'aikatu a Bissau babban birnin kasar, suka kasance a rufe, in banda asibitoci dake yajin aikin tare da jalalo.
Kasar Guniea Bissau dai na fama da rikicin siyasa tun bayan da shugaban kasar, Jose Mario Vaz, ya tsige fira ministansa, Domingos Simoes Pereira, a watan Agusta na 2015.
Tags