Sudan Ta Kudu: An Cimma Yarjejeniya Kan Raba Madafan Iko
(last modified Thu, 26 Jul 2018 06:57:41 GMT )
Jul 26, 2018 06:57 UTC
  • Sudan Ta Kudu: An Cimma Yarjejeniya Kan Raba Madafan Iko

Gwamnati da 'yan tawayen Sudan ta kudu sun cimma yarjejeniya akan raba madafan iko a tsakaninsu

Kamfanin dillancin labarun Faransa  ya ambato ministan harkokin wajen kasar Sudan al-dardari Muhammad Ahmad yana cewa; A karkashin yarjejeniyar Reikh Machar zai koma kan tsohon mukaminsa na mataimakin shugaban kasa.

Ministan harkokin wajen kasar ta Sudan wanda yake magana a wurin bikin rattaba hannu akan yarjejeniyar a birnin Khartum ya kara da cewa; Silva Kiir zai ci gaba da zama a matsayin shugaban kasa shi kuma Reikh Machar a matsayin mataimakinsa na farko.

Har ila yau a karkashin yarjejeniyar an kirkiro mukaman mataimakin shugaban kasa har guda hudu da za a raba su a tsakanin kabilu daban-daban na kasar.

Tun a 2013 ne dai kasar ta fada cikin yakin basasa a tsakanin sojojin da suke biyayya ga shugaban kasa Silva Kiir da kuma mataimakinsa Reikh Machar.