Sudan Ta Kudu: An Cimma Yarjejeniya Kan Raba Madafan Iko
Gwamnati da 'yan tawayen Sudan ta kudu sun cimma yarjejeniya akan raba madafan iko a tsakaninsu
Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato ministan harkokin wajen kasar Sudan al-dardari Muhammad Ahmad yana cewa; A karkashin yarjejeniyar Reikh Machar zai koma kan tsohon mukaminsa na mataimakin shugaban kasa.
Ministan harkokin wajen kasar ta Sudan wanda yake magana a wurin bikin rattaba hannu akan yarjejeniyar a birnin Khartum ya kara da cewa; Silva Kiir zai ci gaba da zama a matsayin shugaban kasa shi kuma Reikh Machar a matsayin mataimakinsa na farko.
Har ila yau a karkashin yarjejeniyar an kirkiro mukaman mataimakin shugaban kasa har guda hudu da za a raba su a tsakanin kabilu daban-daban na kasar.
Tun a 2013 ne dai kasar ta fada cikin yakin basasa a tsakanin sojojin da suke biyayya ga shugaban kasa Silva Kiir da kuma mataimakinsa Reikh Machar.