An Gano Wani Sabon Nau'in Cutar Ebola A Saliyo
Gwamnatin Saliyo, ta sanar da gano wani sabon nau'in cutar Ebola a jikin jemage, shekaru biyu bayan kawo karshen cutar Ebola data kashe mutum sama da 11,000 a yammacin Afrika.
Sanarwar da gwamnatin Saliya ta fitar a jiya Alhamis, ta ce har yanzu babu tabas akan ko sabon nau'in kwayoyin cutar da ake kira ''Bombali'' zai iya rikide wa zuwa cutar Ebola mai kisa.
Haka zalika har yanzu babu masaniya akan ko kwayoyin cutar sun yadu zuwa mutum, ko kuma suna iya haddasa rashin lafiya ga dan adam, amma akwai alamar zai iya kama wasu kwayoyin halitta na mutum, a cewar Amara Jambai, wani babban jami'i a ma'aikatar lafiya ta kasar.
Jami'in ya ci gaba da cewa ana cikin bincike, tare da kira ga jama'ar kasar dasu kwantar da hankulansu, tare da kauce wa cin naman jemage.
A yanzu dai akwai nau'ukan cutar Ebola mabanbanta har guda biyar da suka hada da Zaire, wacce aka fara gano wa a shekara 1976 a tsohuwar kasar Zaire wacce ake kira D.R.Congo a yau.