An Samu Bashin Naira Biliyan 1.6 Domin Biyan Albashin Kananan Hukumomin Abuja
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3250-an_samu_bashin_naira_biliyan_1.6_domin_biyan_albashin_kananan_hukumomin_abuja
Ministan babban birnin tarayyar Najeriya Abuja ya bayar da bashin Naira biliyan 1.6 domin biyan albashin ma'aikatan kananan hukumomin Abuja.
(last modified 2018-08-22T06:58:04+00:00 )
Apr 01, 2016 08:40 UTC

Ministan babban birnin tarayyar Najeriya Abuja ya bayar da bashin Naira biliyan 1.6 domin biyan albashin ma'aikatan kananan hukumomin Abuja.

Bayan kwashe kimanin watanni 8 a jere ma'aikatan kananan hukumomin Abuja ba su samu albashi ba, Ministan babban birnin tarayyar Najeriya Abuja ya bayar da bashin Naira biliyan 1.6 domin biyan albashin nasu na watanni biyu.