An Ceto Bakin Haure 'Yan Afirka Kimanin Dubu Daya A Tekun Bahrum
Masu ayyukan ceto A kasar Spaniya sun ceto sama da bakin haure 'Yan kasashen Afirka kimanin 1,000 daga nutsewa a Tekun Bahrum a cikin kwanaki biyu.
Cikin wata sanarwa da suka fitar , Masu ayyukan ceto na kasar Spaniya sun ce cikin kwanaki biyu sun ceto sama da bakin haure 1,000 daga nutsewa a Tekun Bahrum , da suka fito daga arewacin Afirka a kokarinsu na shiga kasashen Turai.
Da farko masu ayyukan ceton sun fara fitar da mutane 774 da ke cikin jiragen ruwa daban-daban har 52, kamin daga bisani jami'an agajin sun yi nasarar fitar da wasu mutane 206 daga jirage 10 da ke yunkurin kifewa a cikin Teku.
A yanzu dai kasashen Aljeriya da Moroko ne ke zama kofar da bakin hauren Afirka ke bi tun bayan da Libiya ta killace iyakokinta da kasar Italiya.
An kiyasta cewa akalla bakin haure dubu 20 ne suka shiga kasar Spain ta ruwa a shekarar 2018.