Zaben Zimbabwe : Mugabe Ya Ce Zai Goyi Bayan 'Yan Adawa
(last modified Sun, 29 Jul 2018 19:08:10 GMT )
Jul 29, 2018 19:08 UTC
  • Zaben Zimbabwe : Mugabe Ya Ce Zai Goyi Bayan 'Yan Adawa

Tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya sanar da cewar ba zai goyi bayan jam'iyyar Zanu-PF mai mulki ba a zaben shugabancin kasar da za a gudanar.

A zantawarsa da manema labarai a gidansa da ke birnin Harare fadar mulkin kasar Zimbabwe a yau Lahadi: Tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya bayyana cewar ba zai goyi bayan jam'iyyarsa ta Zanu-PF mai mulki ba a zaben shugabancin kasar da za a gudanar, don haka madugun 'yan adawar kasar Nelson Chamisa shi ne gwaninsa.

Robert Mugabe ya zargi gwamnatin shugaba Emmerson Mnangagwa mai ci da cewar gwamnati ce da bata kan doka domin Emmerson Mnangagwa ya dare kan karagar shugabancin kasar ne da karfin bindiga.

A gobe Litinin ne ake sa-ran gudanar da zaben shugaban kasa  a Zimbabwe, inda za a fafata a tsakanin jam'iyyar Zanu-PF mai mulki ta shugaba Emmerson Mnangagwa da babbar jam'iyyar adawa ta kasar ta Movement for Democratic Change "MDC" a takaice da ta tsaida Nelson Chamisa dan shekaru 40 a duniya.