Najeriya : An Aike Da Sojojin 1,000 Da Jiragen Yaki A Zamfara
Shugaba muhammadu Buhari a Najeriya ya bada umurnin aike da jami'an tsaro wadanda suka hada da sojoji yan sanda da kuma mayaka masu sa kai kimani dubu guda zuwa jihar zamfara don magance ayyukan yan bindiga masu kashe mutane a jihar.
Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto kakakin shugaban kasar Garba Shehu ne ya bayyana haka a jiya Lahadi a lokacinda yake ganawa da yan jarida a fadar shugaban kasa. Garba Shehu ya kara da cewa shugaban kasar har'ila yau ya bawa sojojin sama na kasar umurnin su yi amfani da jiragen sama don yakar wadanan yan bindiga.
Kafiun yanzu dai ya ce ba'a amfani da jiragen sama a wajen yakar yan bindigar, amma a halin yanzu an warware matsalar da take hana hakan. Ya ce an tura jiragen yaki zuwa tashar Jiragen saman na katsina daga inda zasu yi aikinsu. Sojojin har'ila yau zasu yi amfani da fasahar zamanio wajen gano inda yan bindigar suke.