An Fara Zaben Shugaban Kasa A Fadin Zimbabwe
Da misalin karfe 7 na safiyar yau litinin aka bude cibiyoyin zabe domin kada kuri'a a zaben shugaban kasa na farko ba tare da Robert Mugabe ba.
Da akwai mutane 23 da za su yi gogayya da juna a cikin zaben na yau. sai dai ana ganin cewa wadanda za su fi yin gogayya da juna su ne shugaba mai ci Emmerson Mnangagwa na jam'iyyar ZANU-PF, sai kuma dan hamayya Nelson Chamisa.
Idan har a karon farko ba a sami wanda ya lashe fiye da rabin kuri'un da aka kada ba, to za a je zagaye na biyu a ranar 8 ga watan Satumba.
Wannan dai shi ne karon farko da ake zaben shugaban kasa a Zimbabwe ba tare da shugaba Robert Mugabe ba wanda ya jagoranci kasar na tsawon shekaru 37. A ranar 21 ga watan Nuwamba na 2017 ne sojojin kasar su ka sauke Mugabe daga mukamin nashi da tilasta masa yin murabus.