Najeriya : An Tsige Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32553-najeriya_an_tsige_shugaban_majalisar_dokokin_jihar_kano
A Najeriya 'yan majalisar dokokin jihar Kano da ke arewacin kasar, sun tsige shugaban majalisar, Alhaji Yusuf Abdullahi Ata daga mukaminsa na shugaban majalsiar jihar.
(last modified 2018-08-22T07:02:10+00:00 )
Jul 30, 2018 10:53 UTC
  • Najeriya : An Tsige Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano

A Najeriya 'yan majalisar dokokin jihar Kano da ke arewacin kasar, sun tsige shugaban majalisar, Alhaji Yusuf Abdullahi Ata daga mukaminsa na shugaban majalsiar jihar.

'Yan majalisar ashirin da bakwai ne daga cikin arba'in suka sanya hannu a kan kudirin tsige Hon. Ata daga mukaminsa a yau Litini.

Dama kafin hakan an shafe dogon lokaci 'yan majalisar na kokarin yin hakan, bisa zargin kakakin majalisar da rashin iya tafiyar da majalisar, da raba kawunan 'ya 'yanta da kuma zubar da kimar majalisar a idon al'umma, zarge zarge da ya musunta.

Ko a watan  Mayun da ya gabata ma saida jami'an 'yan sanda suka yi wa majalisar kawanya, don hana 'yan majalisar shiga a kokarinsu na tsige shugaban.

A yanzu dai 'yan majalisar sun nada Kabiru Alhassan Rurum, wanda shi ne mataimakin Honorobul Ata din kafin a sauke shi, wanda shi kuwa idan ana tune ya yi murabus daga shugabancin majalisar a watan Yilin bara, bayan zarginsa da aikata laifuka da suka shafi cin hanci.