An Samu Kusantuwa Tsakanin Eritrea Da Somaliya
Jul 31, 2018 06:46 UTC
Shugaban kasar Somalia, Mohamed Farmajo, ya kammala wata ziyarar aiki ta kwanaki uku a makofciyar kasar Eritrea, wacce aka bayyana da mai matukar tarihi.
Kasashen biyu dai sun shafe kusan shekaru 15 basu da huldar dflomatsiyya.
Amma a yayin wannan ziyarar kasashen biyu sun kulla yarjejeniyar maido da huldar diflomatsiyya da musayar jakadu a tsakaninsu.
An dai sanya hannu kan wannan yarjejeniya ce tsakanin shugaban kasar Eritrea Issaias Afeworki, da kuma takwaransa na Somalia, Mohamed Abdullahi Mohamed.
Tags