Zimbabwe : Manyan 'Yan Hammaya Na Ikirarin Lashe Zabe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32564-zimbabwe_manyan_'yan_hammaya_na_ikirarin_lashe_zabe
'Yan hammaya a Zimbabwe, sun fara ikirarin lashe zaben shugaban kasar da aka kada kuri'arsa a jiya Litini.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Jul 31, 2018 11:17 UTC
  • Zimbabwe : Manyan 'Yan Hammaya Na Ikirarin Lashe Zabe

'Yan hammaya a Zimbabwe, sun fara ikirarin lashe zaben shugaban kasar da aka kada kuri'arsa a jiya Litini.

Bangarorin da suka hada da shugaba Emmerson Mnangagwa da kuma babban abokin hamayyarsa, shugaban matasa na jam'iyyar adawa ta MDC, Nelson Chamisa, duk sun bayyana kansu a matsayin na gaba a sakamakon zaben.

Wannan zaben dai shi ne irinsa na farko da aka gudanar tun bayan hambarar da mulkin tsohon shugaban kasar Robert Mugabe, kuma an samu fitowar jama'a sosai a zaben.