Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Ya Bar Jam'iyyar APC
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32571-shugaban_majalisar_dattijan_najeriya_ya_bar_jam'iyyar_apc
Shugaban majalisar datijjan Najeriya, Bukola Saraki, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC mai mulki a kasar.
(last modified 2018-08-22T07:02:11+00:00 )
Aug 01, 2018 00:59 UTC
  • Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Ya Bar Jam'iyyar APC

Shugaban majalisar datijjan Najeriya, Bukola Saraki, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC mai mulki a kasar.

Saraki ya bayana hakan ne a shaffinsa na Twitter jiya Talata, yana mai cewa : "Ina sanar da 'yan Najeriya cewa bayan tattaunawa, na yanke shawarar fita daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kafin hakan dama an jima ana ta yayata jita jitan cewa Sarakin zai bar jam'iyyar ta APC.

Sai dai kawo yanzu Sarakin bai bayyana jam'iyyar da zai koma ba tukunna. 

Wannan dai na zuwa ne 'yan kwanaki kadan bayan da wasu sanatoci daga jam'iyyar APC suka canza sheka zuwa babbar jam'iyyar adawa ta PDP.