Wata Kotun Abuja Ta Fitar Da Sammacin Kama Shugaban Hukumar Zabe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32582-wata_kotun_abuja_ta_fitar_da_sammacin_kama_shugaban_hukumar_zabe
Wata kotun tarayya a Abuja ta fidda sammashin kama shugaban hukumar zaben kasar a yau Laraba
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Aug 01, 2018 14:29 UTC
  • Wata Kotun Abuja Ta Fitar Da Sammacin Kama Shugaban Hukumar Zabe

Wata kotun tarayya a Abuja ta fidda sammashin kama shugaban hukumar zaben kasar a yau Laraba

Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto Justice Stephen Pam yana fadar cewa shugaban hukumar zaben Prof. Yakubu Mahmoud yana rena umurnin kotu shi ya sa ya bada sammashin kama shi.

Labarin ya kara da cewa Justice Pam ya bukaci shugaban hukumar zaben ya zo kotun har sau ukku amma ya ki amsa kiransa. A ranar 15 ga watan Yulin da ya gabata ne Justice Stephen Pam ya bada umurni na ukku don ganin shugaban hukumar zaben ya amsa kiransa don amsa tambayoyi kan wadanda suka shiga takarar neman shugabancin na jam'iyyar PDP na jihar Anambra, amma ya ki amsawa.

Labarin bai bayyana dalilan da suka hana shugaban hukumar zaben amsa kiran kotun ba.