Yan Adawa A Zimbabwe Na Zanga Zanga Kin Amincewa Da Sakamakon Zabe
(last modified Wed, 01 Aug 2018 19:00:09 GMT )
Aug 01, 2018 19:00 UTC
  • Yan Adawa A Zimbabwe Na Zanga Zanga Kin Amincewa Da Sakamakon Zabe

Dubban magoya bayan jam'iyyar adawa mafi girma a kasar Zimbabwe sun fito zanga zanga a birnin Harare babban birnin kasar inda suke nuna rashin amincewarsu da sakamakon zaben majaliasar dokokin wasar wanda ya nuna cewa jam'iyya mai mulki ce ta sami nasara a cikinsa.

Kamfanin dillanin labaran AFP na kasar Faransa ya bayyana cewa jami'an tsaro sun harba amfani da albarusan yaki kan masu zanga zanga wanda ya kai ga rasuwar mutum guda. 

Sakamakon zaben majalisar dokokin kasar ya nuna cewa jam'iyyar "National Union of Zimbabwe-National Front" mai mulki ta lashe kujeru 145 daga cikin kujeru 210 na majalisar dokokin kasar, a yayinsa jam'iyyar yan adawa mafi girma Democratic change" ta sami kujeru 60 ne kacal. 

A ranar Litinin 30 ga watan Yuli ne aka gudanar da zaben majalisar dokoki da kuma na shugaban kasa a kasar ta Zimbabwe, sai har yanzun hukumar zaben kasar basa bayyana sakamakon zaben shugaban kasa wanda shi ma ake zaton shugaban mai ci  Emmerson Mnangagwa zai lashe zaben, a yayin da dan takarar jam'iyyar adawa mafi girma Nelson Chamisa zai zama na biyu.