Zimbabwe : Tarzoma Ta Barke Bayan Sanar Da Sakamakon Zaben 'Yan Majalisa
(last modified Thu, 02 Aug 2018 07:49:47 GMT )
Aug 02, 2018 07:49 UTC
  • Zimbabwe : Tarzoma Ta Barke Bayan Sanar Da Sakamakon Zaben 'Yan Majalisa

Hukumar zaben kasar Zimbabwe ta sanar da cewa: Jam'iyyar Zanu-PF mai mulki a kasar ita ce ta samu mafi yawan kujerun 'yan Majalisun Dokokin Kasar a zaben da aka gudanar a ranar Litinin da ta gabata.

Hukumar zaben Zimbabwe a jiya Laraba ta sanar da cewa: Jam'iyyar Zanu-PF mai mulki a kasar ta samu nasarar lashe mafi yawan kujerun Majalisar Dokokin Kasar, inda ta samu kashi biyu cikin uku na kujerun Majalisar, duk da cewa ta jinkirta sanar da sakamakon zaben shugaban kasar lamarin da ya fusata magoya bayan babbar jam'iyyar adawar kasar ta Movement for Democratic Change "MDC" a takaice.

Rahotonni sun bayyana cewa: A dauki ba dadi da aka yi tsakanin jami'an tsaron kasar Zimbabwe da gungun 'yan adawar jam'iyyar MDC da suka fito kan manyan hanyoyin birnin Harare fadar mulkin kasar domin bayyana rashin amincewarsu da sakamakon zaben akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu.

Madugun 'yan adawar Zimbabwe Nelson Chamisa ya zargi jam'iyyar Zanu-PF da tafka magudi a zabukan da aka gudanar a kasar tare da furta da'awar cewa shi ne ya lashe zaben shugabancin kasar.