Nigeriya: Ruwa Ya Ci Rayukan Mutane 21 A Jihar Sokoto
Kimanin mutane 21 ne suka rayukansu sanadiyar wani hadari da kwale-kwale ya yi a kogin Gandi na jihar Sokoto dake shiyar arewa maso gabashin Najeriya.
Rahotanni dake fitowa daga jihar Sokoto na cewa a jiya alhamis wani kwale-kwale dauke da 'yan gudun hijra na jihar Zamafara ya yi hadari a cikin ruwan Kogin Ganda, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 21 cikin akwai mata 17.
Hukumomin jahar Sokoto sun tabbatar da aukuwar lamarin sannan sun cewa mutanen suna kan hanyarsu ce ta zuwa kauyensu mai suna Gidan-Kari yayin da kwale-kwalen ya kife a kogin.
Ya zuwa yanzu ba a bayyana dalilin da ya jawo hadarin ba tukunna, amma ana yawan samun hadarin kwale-kwale saboda dibar mutane fiye da kima da yawan torokon ruwa da rashin kula da jiragen ruwan yadda ya kamata da kuma rashin kyauwun kogunan da suke bi.