Salva Kiir: Dukkanin Bangarori Za Su Yi Aiki Da Yarjejeniyar Sulhu
Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir ya jaddada cewa, dukkanin bangarori na gwamnati da kuma 'yan tawaye za su yi aiki da yarjejeniyar sulhu da za a rattaba wa hannu a gobe Lahadi.
Shafin yada labarai na Al-nashrah ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai yau a birnin Juba, shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir ya tabbatar da cewa, a wannan karon yarjejeniyar sulhu da za a rattaba hannu a kanta za ta yi karko, domin dukkanin bangarorin yarjejeniyar za su yi aiki da ita.
Ya ce ba shi da wata tababa a kan cewa, gwamnati da bangaren 'yan tawaye a wannan karon ba su da wata matsala kan abin da suka cimma matsaya a kansa, domin kuwa abin da dukkanin bangarorin suka amince da shi ne yarjejeniyar ta kunsa kuma a kansa ne za a rattaba hannu.
A gobe ne dai shugaba Salva Kiir da kuma madugun 'yan tawayen Sudan ta kudu Riek Macher za su hallara a birnin Khartum na kasar Sudan, domin rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhu tare da halartar shugaban Sudan Umar Hassan Albashir.