Mataimakin Gwamnan Jihar Kano A Tarayyar Najeriya Ya Ajiye Aikinsa
Mataimakin gwamnan jihar Kano Alhaji Hafiz Abubakar ya ajiye aikinsa a jiya Asabar bayan da ya bayyana cewa ba zai iya ci gaba da aiki tare da gwamnatin da yake da sabanin ra'ayi kan yadda za'a tafiyar da ita ba.
Jaridar Primiumtimes ta Najeriya ta sami kofin takardan ajiye aikin mataimakin gwamnatin jihar Kanom daga wajen Abdulwahab Ahmad mai magana a madadin mataimakin gwamnan.
Alhaji Hafizu dai na kusa da tsohon gwamnan jihar Kano Senata Rabiu Musa Kwankwaso ne, ya bayyana cewa ya sha samun sabani da gwamnan mai ci Alhaji Abdullahi Ganduge a kann lamuran tafiyar da gwamnati amma gwamnan baya ganin irin wahalan da yake sha.
Ana saran Alhaji Hafiz Abubakar zai koma jam'iyyar PDP a cikin yan kwanaki masu zuwa inda zai hadu da sauran yan jam'iyyar APC da suka fice daga ita a cikin yan makonnin da suka gabata daga cikinsi har da shi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Kakakin gwamnan Jihar Kano ya tabbatarwa jaridar Primiumtime isar wasikar barin aikin na mataimakin gwamnan a yau Lahadi, amma ya ce bai san cewa ko gwamnan ya amince da bukatar ba.