Jam'iyar Adawa Ta Ki Amincewa Da Sakamakon Zabe A Zimbabwe
Babbar jam'iyyar adawa ta Zimbabuwe MDC, ta bayyana cewa za ta fitar da wata sanarwa kan matakin da za ta dauka na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a makon da ya gabata a gaban kuliya.
Wani kusa a Jam'yyar adawar ta Movement for Democratic Change Nkululeko Sibanda ya zargi jami'an tsaron kasar da aikata rashin gaskiya a yayin da ya zargesu da kai farmaki a gidajen magoya bayan 'yan adawa bayan zanga-zangar nuna kin amincewa da sakamakon zaben da 'yan adawar suka yi.
Sibanda ya nunar da cewa wasu mambobin jam'iyyarsu ta MDC ma na buya ne saboda gudun abin da kaje ya zo, kana wasu ba a ma san inda suke ba.
Hukumar zaben kasar ta Zimbabuwe ZEC dai ta ayyana Shugaba Emmerson Mnangagwa a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 30 ga watan Yulin da ya gabata da al'ummar Zimbabuwen suka gudanar, a karkashin da jam'iyyarsa ta ZANU-PF mai mulki, sai dai 'yan adawa sun yi zargin an tafka magudi.