Ivory Coast : Ouatara Ya Yi Wa Matar Gbagbo Afuwa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32664-ivory_coast_ouatara_ya_yi_wa_matar_gbagbo_afuwa
Shugaba Alassane Ouatara ya yi wa mutane 800 afuwa ciki har da matar tsohon shugaban kasar, Simone Gbagbo.
(last modified 2018-08-22T07:02:13+00:00 )
Aug 07, 2018 06:20 UTC
  • Ivory Coast : Ouatara Ya Yi Wa Matar Gbagbo Afuwa

Shugaba Alassane Ouatara ya yi wa mutane 800 afuwa ciki har da matar tsohon shugaban kasar, Simone Gbagbo.

Sauren kuma sun hada wasu jiga jigen 'yan siyasa na kusa da tsohuwar gwamnatin shugaba Laurent Gbagbo, wanda yanzu haka shi yake a hannun kotun hukuntan mayan laifuka ta duniya ICC.

Mista Ouatara ya bayyana hakan ne a cikin jawabinsa ga al'ummar kasar na jajibirin cika shekarau 58 da samun 'yancin kai na kasar.

Matakin dai ya zo wa da jama'ar kasar da dama a ba zata, a daidai lokacin da ake tunanin kasar za ta iya fadawa cikin wani sabon rikicin siyasa.

Dama kafin hakan an yi wa wasu fursuna 500 afuwa.