Mukaddashin Shugaban Kasa Najeriya Ya Tube Shugaban Hukumar DSS Lawan Daura
Mukaddashin shugaban kasan Najeriya Yemi Osinbajo ya tube shugaban hukumar yansandan ciki ta DSS Lawal Daura daga mukaminsa
Tashar talabijin ta Channeltv a najeriya ta bayyana cewa mukaddashin shugaban kasar ya bayyana haka ne a wata sanarwan da babban mataimakinsa a bangaren yada labarai ya sanyawa hannu a yau Talata.
Rahoton ya kara da cewa tuni an bukaci tsohon shugaban na DSS ya mika ikon hukumar ga babban jami'an a hukumar. Labarin ya kara da cewa a lokacin fidda wannan sanarwan dai tsohon shugaban hukumar ta DSS Lawan Daura da kuma babban Spetan yansanda Ibrahim Idris suna tattaunawa a kebe da mukuddanshin shugaban kasa a fadar shugaban kasa.
An sallami Daura daga mukaminsa ne yan sa'o'i bayan da jami'an hukumar ta DSS suka rufe kofar shiga majalisar dokokin kasar, suka kuma hana yan majalisa, da yan jaridu da kuma sauran ma'aikatan majalisar shiga cikinsa na wani lokaci.
Amma daga karshe jami'an tsaro na DSS sun kawo karshen hana shiga majalisar bayan da labarin tsige shugaban nasu ya isa kunnensu.