Ambaliyar Ruwa Ta Ci Rayukan Mutum 22 A Nijer
Ministan dake kula da Ayyukan Agaji da Bala'i na dabi'a a Nijer ya sanar da cewa ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake yi a kasar ya janyo ambaliyar ruwa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 22 sannan wasu da dama sun rasa mahalinsu.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Ministan kula da ayyukan agaji gami da bala'uka na dabi'a na jamhoriyar Nijer Laouan Magadji a jiya laraba na cewa daga ranar 6 ga watan Augusta, sama da mutun dubu 6 ne matsalar ambaliyar ruwar ta shafa a fadin kasar
Magadi ya ce ambaliyar ruwa ta rusa sama da gidaje dubu uku ,ta kuma ci filayen noma sama da hekta dubu, sannan kuma da tafi da duban dabbobi na al'ummar kasar.
Ministan ya kara da cewa matsalar ta fi shafar kudancin kasar, a birnin Yamai fadar milkin kasar kimanin gidaje dubu biyu ne suka rushe.
Kafin wannan bala'i dai, dama MDD ta gargadi mahukuntan kasar ta Nijer game da ambaliyar ruwan da za a fuskanta a wannan shekara.