Sudan Ta Kudu : Salva Kiir Ya Yi Wa 'Yan Tawaye Afuwa
(last modified Thu, 09 Aug 2018 14:52:23 GMT )
Aug 09, 2018 14:52 UTC
  • Sudan Ta Kudu : Salva Kiir Ya Yi Wa 'Yan Tawaye Afuwa

Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir, ya sanar da yin afuwa ga dukkan 'yan tawayen kasar, ciki har da tsohon mataimakinsa kana babban abokin hammayarsa Riek Mashar.

An dai sanar da matakin ne a gidan talabijin din kasar, inda aka ce shugaban kassar, ya yi afuwa ga jagoran kungiyar 'yan tawayen kasar ta SPLM, Dr Riek Mashar Teny, da kuma wasu gungu dake adawa da gwamnatin Sudan ta Kudun tun daga shekara 2013 zuwa yanzu.

Wannan sanarwar dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da gwamnatin kasar da gungun 'yan tawayen kasar suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar raba iko a Khartum babban birnin kasar Sudan, domin kawo karshen yakin basasar da aka kwashe kusan shekaru biyar ana yi, wanda kuma ya yi sanadin mutuwar dubun dubatar mutane a kasar ta Sudan ta Kudu. 

An dai cimma yarjejeniyar ce a shiga tsakanin kungiyar IGAD data hada kasashen yankin.

A watan Disamba na 2013 ne fada ya barke tsakanin dakaruun gwamnati da kuma wadanda ke biyaya ga Riek Mashar, bayan zargin wani yunkirin juyin mulki da Shugaba Kiir ya yi wa mataimakin nasa, batun da shi Mashar din ya musunta.