WHO: An Fara Allurar Riga Kafin Ebola A D.R Congo
Hukumomin lafiya a lardin Arewacin Kivu na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, sun fara gudanar da alluran rigakafin cutar Ebola mai saurin kisa.
Bayanai daga hukumar lafiya ta duniya WHO sun ce an fara gudanar da rigakafin ne a yankuna da suka fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar.
An kuma fara da yi wa ministan lardin, da jami'in tsare tsaren aikin rigakafin wannan allura, a aikin da ake fatan fadada shi, ta yadda dukkanin wadanda suka dace a yi musu allurar za su amfana.
Kafin hakan dai hukumomin Lafiya a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo sun sanar da cewar an sake samun Karin mutane 4 da suka rasa rayukan su sakamakon kamuwa da cutar Ebola, makwanni biyu bayan an sanar da magance cutar da ta hallaka mutane 33.
Mutane 43 ne ake zargin sun kamu da cutar, yayinda aka tabbatar da 16 daga ciki, sai kuma 27 wadanda har yanzu ake da shakku kan su.