'Yan Boko Haram Sun Kashe Sojoji 15 A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32713-'yan_boko_haram_sun_kashe_sojoji_15_a_najeriya
A Wani Harin Ba Zata da mayakar boko haram suka kaiwa sojojin Najeriya a garin Damasak na jihar Borno, Akalla sojoji 15 da wani jami'in hukumar agaji ne suka rasa rayukansu
(last modified 2018-08-22T07:02:13+00:00 )
Aug 10, 2018 14:26 UTC
  • 'Yan Boko Haram Sun Kashe Sojoji 15 A Najeriya

A Wani Harin Ba Zata da mayakar boko haram suka kaiwa sojojin Najeriya a garin Damasak na jihar Borno, Akalla sojoji 15 da wani jami'in hukumar agaji ne suka rasa rayukansu

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto wani jami'in hukumar agajin gaggawa ta NEMA da ya nemi a sakaye sunansa, na cewa mayakan 'yan boko haram din sun bude wuta da bindigogi kan sojojin da jami'in na su guda a yayin da suke tsakiyar aikin katange wani yanki a garin na Damasak.

Harin da aka kai ranar  Larabar da ta gabata ya kasance  mafi muni a baya bayan nan a jihar da ta rasa mutum fiye da dubu talatin a sanadiyar ayyukan ta'addanci. 

Mayakan na Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare nan da can duk kuwa da kokarin da hukumomin kasar ke yi don ganin an dakile ayyukansu da kuma tabbatar da tsaro a yankin gabanin babban zaben kasar.

Alkalumma dai sun nuna cewa mutane samda da 20,000 ne suka rasa rayukansu, kana wasu miliyan 2,3 suka rasa muhallansu tun dai bayan da kungiyar boko haram ta soma kai hare harenta a Najeriya a cikin shekara 2009.