Chamisa Ya Shigar Da Kara Kan Sakamakon Zaben Kasar Zimbabwe
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa mafi girma a kasar Zimbabwe Nelson Chamisa ya shigar da kara a gaban kotun kundin tsarin mulkin kasar a jiya Jumma'a inda yake kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar wanda shugaban mai ci ya lashe.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto lawayan Nelson Chamisa, Tnabano Mpofu yana cewa ya bukacin kutun kundin tsarin mulkin kasar da ta bayyana wanda ya lashe zaben shugaban kasa na gaskiya a zaben ranar 30 ga watan Yulin da ya gabata ko kuma ta soke zaben a mataki na biyu, ta kuma bukaci a sake shi.
Da haka kuma aka dakatar da bukin rantsar da shugaban kasa Emmerson Mnangagwa a gobe lahadi har zuwa lokacinda kotun zata kammala shari'ar. A cikin kundin tsarin mulkin kasar Zimbabwe dai duk wanda yake da korafi a sakamakon zabe dole ne a shigar da kara a gaban kotun kundin tsarin mulkin a cikin mako guda bayan sanar da sakamakon zaben. Sannan ita kuma kotun dole da yanke sharia a kan batun a cikin makonni biyu. Shugaban Emmerson Mnangagwa dai ya ce a shirye suke su kare zaben da aka yi masa a gaban kotun.