Borno: Kananan Yara 33 Sun Mutu A Sansanin 'Yan Gudun Hijira
Kungiyar likitoci ba tare da iyaka ba ta kasa da kasa ce ta sanar da mutuwar yaran saboda rashin abinci mai gina jiki
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ambato majiyar kungiyar likitocin na fada a yau juma'a cewa: Yaran 33 sun mutu ne a cikin makwanni biyu da su ka gabata a yankin Bama da ke jahar Borno a arewa masu gabacin kasar.
Bayanin likitocin ya kara da cewa: Kananan yaran suna rayuwa cikin matsananci yanayi a cikin sansanin yan gudun hijirar, kuma ba sa kula da su ko kadan.
Sansanin 'yan gudun hijirar da ke Bama na mutanen da rikicin yakin Boko Haram ya rutsa da su ne.
Rikicin wanda ya fara tun 2009 ya zuwa yanzu ya ci rayukan mutane fiye da 20,000, ya kuma haifar da 'yan gudun hijira fiye da miliyan 2 da 600,000.