An Fara Sayar Da Fom Din Takarar Shugabancin Kasa A Najeriya
Hukumar zaben Najeriya ta sanar da cewa, ta fara sayar da fom din tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben shekara ta 2019.
A cikin wani bayani da hukumar zaben ta Najeriya INEC ta fitar, ta bayyana cewa, dukkanin jam'iyyun da aka yi wa rijista suna da damar su gudanar da zabukan fitar da gwani, tare da mika mata sunayen 'yan takararsu daga zuwa watan Oktoba.
Hukumar INEC ta kara da cewa, dole ne jam'iyyu su kiyaye dukkanin ka'idojin da aka gindaya da suka shafi zaben.
A cikin watan Fabrairun shekara ta 2019 ne dai ake sa ran za a gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriya, inda jam'iyyar APC mai mulki ta sanar da shugaba Buhari a matsayin dan takararta, wanda zai kara da sauran 'yan takara da za su tsaya a zaben.
 
							 
						 
						