An Karfafa Matakan Tsaro a Birnin Harare Na Zimbabwe
(last modified Thu, 23 Aug 2018 11:58:12 GMT )
Aug 23, 2018 11:58 UTC
  • An Karfafa Matakan Tsaro a Birnin Harare Na Zimbabwe

Bayan da Babban alkalin kasar Zimbabuwe ya sanar da cewa zai yanke hukunci kan zaben shugaban kasar a gobe juma'a, aka baza jami'an tsaro a birnin harare.

Jami'an tsaro dai sun kewaye bangarori daban-daban na Harare babban birnin kasar ta Zimbabuwe cikin shirin ko ta kwana, yayin da kotun zaben ta fara sauraron karar da jam'iyyar adawa ta shigar gabanta, bisa zargin aringizon kuri'a a yayin bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da ya gudana a watan Yulin da ya gabata.

'Yan adawar dai sun bayyana zaben da cewar yana cike da kura-kurai da kuma magudi a wasu mazabun, tare da neman a sake sabon zabe a kasar. Wannan zabe dai shi ne na farko a kasar bayan da aka tilasta wa tsohon shugaban kasar Robert Mugabe sauka daga kan karagar mulki.