Sudan: Al-Bashar Ya Yi Alkawarin Kawo Gyara A Tattalin Arzikin Kasar
Shugaba Omar Al-Bashir na kasar Sudan ya yi da'awar cewa rage jami'an Diplamasiyar kasar da ya yi a kasashen waje zai taimaka wajen rage kudaden da kasar ke kashewa.
Kamfanin dillancin labaran Sudan ya nakalto shugaba Omar Al-Bashir jiya Laraba na cewa zai yi iya kokarinsa wajen gyara da canji a tafarkin Siyasa, tattalin arziki a zamantakewa a kasar da nufin amsa bukatun al'ummar kasar.
Shugaban kasar ta Sudan ya ce zai sanya ido sosai a ma'aikatun kasar domin karya lagon masu yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa da wadanda suke wawushe dukiyar al'ummar kasar ta Sudan.
Wannan alkawari na zuwa ne bayan da binciken jin ra'arin Al'umma ya nuna cewa kashi 92% na cikin al'ummar kasar na adawa na yin takarar shugaba Al-Bashir a zaben 2020.
Tun a shekarar 1993 ne Shugaba Al-Bashir ke kan karagar milkin kasar Sudan, sannan kuma ana zarginsa da hannu da kashe mutane kimanin dubu 200 a rikicin yankin Darfur, wanda haka ne ma ya sanya kotun hukunta manya laifuka ta kasa da kasa ke neman a meka mata shi domin ya fuskanci hukunci.