Gyaran Fuska A Majalisar Ministocin Kasar Mauritaniya
Apr 02, 2016 05:23 UTC
Shugaban kasar Mauritania Muhammad Wuld Abdulaziz ya gudanar da wani gyaran fuska a majalisar dokokin kasar.
A wata sanarwa da ofishin shugaban kasar ta Mauritania ya fitar a jiya, ya sanar da cewa shugaba Muhamamd Wuld Abdulaziz ya gudanar da wani garambawul a majlaisar ministocin kasar wanda ya shafi ma'akatu daban-daban da hakan ya hada har da canja ministocin harkokin waje da na cikin gida.
Shugaban na Mauritania dai yana fiuskantar matsin lamba mai tsanani daga bangaren 'yan adawa na kasar, inda wasu daga cikinsu suka yi watsi da gayyatar da ya yi musu domin tattaunawa kan kafa gwamnatin hadin kan kasa.
Tags