An Karyata Jita-Jitan Takarar Madugun 'yan Adawar Kasar D/Congo.
(last modified Sat, 25 Aug 2018 05:24:04 GMT )
Aug 25, 2018 05:24 UTC
  • An Karyata Jita-Jitan Takarar Madugun 'yan Adawar Kasar D/Congo.

Kwamitin zabe mai zaman kansa na jamhoriyar D/Congo ya karyata jita-jitan cewa madugun 'yan adawar kasar JEAN-PIERRE BEMBA zai tsaya takarar shugaban kasa.

Cikin wani rahoto da kamfanin dillancin labaran Reuteus ya fitar a jiya juma'a ya ambato sunan Pierre Bemba da wasu tsofin ministocin kasar biyu a jerin sunayen da hukumar zaben ta amince da takararsu a zaben shugaban kasar da zai gudana a karshen wannan shekara.

Bemba dai ya kwashe shekaru da dama a gidan yarin birnin Hague bisa laifin yaki, kuma a watan Avrilun da ya gabata ne ya dawo Kinshasa babban birnin Kasar D/Congo, inda wasu ke ganin cewa Mista Bemba ya dawo gida ne domin ya tsaya takarar shugabancin kasar.

Har ila yau ana ganin Mista Jen-Pierre Bemba zai samun goyon baya daga Shugaba mai ci, Joseph Kabila.