Sudan Ta Kudu Ta Ci Gaba Da Hakon Danyen Man Fetur
(last modified Mon, 27 Aug 2018 16:53:20 GMT )
Aug 27, 2018 16:53 UTC
  • Sudan Ta Kudu Ta Ci Gaba Da Hakon Danyen Man Fetur

Gwamnatin kasar Sudan ta kudu ta dawo da hakar danyen man fetur a kasar da kuma tura shi zuwa kasar Sudan ta domin fitar da shi zuwa kasashen ketare.

Tun a jiya ne dai aka aka fara aikin tura danyen mai ta hanyar bututu daga Sudan ta kudu zuwa kasar Sudan, inda aka tura ganga dubu 20 a tashin farko.

An samu nasarar ci gaba da ayyukan hakon danyen man ne  Sudan ta kudu, bayan samun daidaito tsakanin bangarorin da suke fada da juna a kasar.

An fara hakar ganga 130,000 a kowace rana, wanda ake sa ran zai zarta zuwa ganga 210,000 a kowace rana zuwa karshen shekarar da muke ciki.