An Kai Hari Kan Barikin Jami'an Tsaron Jandarma A Burkina Faso
(last modified Wed, 29 Aug 2018 06:41:56 GMT )
Aug 29, 2018 06:41 UTC
  • An Kai Hari Kan Barikin Jami'an Tsaron Jandarma A Burkina Faso

Jami'an tsaron kasar Burkina Faso sun sanar da mutuwar jami'an tsaro 8 a wani hari da wasu gungun 'yan ta'adda suka kai barikin jami'an tsaron Jandarma a gabashin kasar

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa a daren litinin wayewar jiya talata,wasu gungun 'yan ta'adda dauke da makamai sun kai hari barikin jami'an tsaron Jandarma na Pama dake gabashin kasar.

Majiyar tsaron kasar ta sanar da cewa 'yan ta'adda sun kashe jami'an jandarma guda 8 sannan kuma sun gone barikin kurmus.

A yayin da maharan suka isa barkin,  jami'an Jami'an jandarmar sun nemi agaji daga garin takwarorinsu na garin Fada N'Gourma, to saidai kafin isar sojojin agajin, 'yan ta'addar sun gudu.

Barikin jami'an tsaron jandarma na Pama na da nisa kilomita sama da dari daga garin Fada N'Gourma na gabashin kasar.

Tun a shekarar 2015 ne kasar Burkina Faso ta fara fuskanta hare-haren ta'addanci a arewaci, tsakiya da kuma gabashin kasar.