An Cimma Yarjejjeniyar Tsaro Tsakanin Birtaniya Da Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32970-an_cimma_yarjejjeniyar_tsaro_tsakanin_birtaniya_da_najeriya
Yayin ziyarar da Piraministan Kasar Birtaniya ta Kai Najeriya , kasashen biyu sun cimma yarjejjeniyoyi da dama ciki harda yarjejjeniyar tsaro
(last modified 2018-08-30T07:55:15+00:00 )
Aug 30, 2018 07:55 UTC
  • An Cimma Yarjejjeniyar Tsaro Tsakanin Birtaniya Da Najeriya

Yayin ziyarar da Piraministan Kasar Birtaniya ta Kai Najeriya , kasashen biyu sun cimma yarjejjeniyoyi da dama ciki harda yarjejjeniyar tsaro

Bayan ganawarta da Shugaba Buhari na Najeriya, a jiya laraba, Firaministar kasar Birtaniya Theresa May ta bayyana cewa kasashen biyu na fuskantar matsalar tsaro irin guda kamar na kungiyoyin 'yan ta'adda da kuma masu safarar mutane, inda ta sha alwashin cewa za ta hada kai da hukumomin Najeriya wajen yakar masu safarar mutane zuwa kasashen Turai.

Har ila yau kasashen biyu sun cimma yarjejjeniyar aiki tare a bangaren tattalin arziki.

Wannan ziyara ta shugabar gwamnatin Birtaniya a Najeriya na zuwa ne a yayin da ya rage kasa da shekara guda a gudanar da zabe a kasar, inda shugaba Buhari dake neman a sake zabensa a karo na biyu ke shan suka na ganin ya kasa cika alkawarin da ya dauka da farfado da tattalin arzikin kasar da kuma kawo karshen matsalar boko haram a arewa maso gabashin kasar.