Sudan Ta Kudu: Machar Ya Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Sulhu Ta Karshe
Madugun 'yan tawayen kasar Sudan ta kudu Riek machar ya sanya hannu kan yarjejeniyar sulhu ta karshe wadda za ta kawo karshen yakin basasar da kasar ta yi fama da shi.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a daren jiya Alhamis ne Riek machar ya rattaba hannu kan yarjejeniyar a birnin Khartum.
A zaman da aka gudanar a kwanakin baya a birnin na Khartum an cimma matsaya kan dukkanin abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa, inda shugaba Salva Kiir ya sanya hannu a kanta, amma Riek Machar yaki ya sanya hannu, inda ya ce sai sun kara yin shawara, inda a daren jiya ya rattaba hannu a kan wannan yarjejeniya.
Bisa ga abin da yarjejeniyar ta kunsa dai Riek Machar zai koma kan matsayinsa na mataimakin shugaban kasa, da kuma raba madafun iko a tsakanin dukkanin bangarorin biyu, da kuma sauran bangarorin da suke a cikin yarjejeniyar.