Waziriyar Kasar Jamus Ta Kai Ziyarar Aiki Tarayyar Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32989-waziriyar_kasar_jamus_ta_kai_ziyarar_aiki_tarayyar_najeriya
Waziriyar kasar Jamus Angela Merkel ta kai ziyarar aiki tarayyar Najeriya inda kasashen biyu suka rattaba hannu kan yerjeniyoyi da dama.
(last modified 2018-09-01T01:57:05+00:00 )
Sep 01, 2018 01:57 UTC
  • Waziriyar Kasar Jamus Ta Kai Ziyarar Aiki Tarayyar Najeriya

Waziriyar kasar Jamus Angela Merkel ta kai ziyarar aiki tarayyar Najeriya inda kasashen biyu suka rattaba hannu kan yerjeniyoyi da dama.

Jaridar Daily Trust ta nakalto shugaban Mohammadu Buhari yana yabawa Angela Merkel kan yadda gwamnatin kasar Jamus take mutunta yan najeriya da suke gudun hijira a kasarta.

Banda shugaban yayi alkawarin kara kyautata dangantakar Najeriya da kasar Jamus a bangarorin tsaro, ilmi da kuma samar da ayyukan yi. 

A nata bangaren waziriyar kasar Jamus ta ce gwamnatin Jamus a shirye take ta fadada dangantaka da tarayyar Najeriya. sannan ta ce yerjeniyoyi ukku da aka rattabawa hannu a jiya somin tabi ne na wasu da zasu zo nan gaba. 

Yerjeniyoyin da aka rattabawa hannu dai sun hana da na harhada motocin Volkswagen a Najeriya, da samar da iri da kuma injunan sarrafa kayakin gona da kuma na harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu.