Kananen Yara Miliyan 5 Suka Hallaka Sanadiyar Yaki Da Rikici A Afirka
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32998-kananen_yara_miliyan_5_suka_hallaka_sanadiyar_yaki_da_rikici_a_afirka
Kimanin kananen yara miliyan 5 ne suka rasa rayukansu sanadiyar yaki da kuma rikicin da ya auku a kasashen Afirka tsahon shekaru 20 da suka gabata
(last modified 2018-09-01T14:33:10+00:00 )
Sep 01, 2018 14:33 UTC
  • Kananen Yara Miliyan 5 Suka Hallaka Sanadiyar Yaki Da Rikici A Afirka

Kimanin kananen yara miliyan 5 ne suka rasa rayukansu sanadiyar yaki da kuma rikicin da ya auku a kasashen Afirka tsahon shekaru 20 da suka gabata

Wani binciken masana ya ce yake-yaken da aka gwabza a Afirka sun yi sanadiyyar mutuwar yara sama da miliyan 5 a cikin shekaru 20, saboda yadda tashin hankalin ya hana su zuwa asibiti domin samun kulawar da ta dace.

Rahotan binciken da aka wallafa a Jaridar Lafiya ta The Lancet ta yi nuni da yadda tashin hankalin da aka gani a kasashen Najeriya da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo tsakanin shekarar 1995 zuwa shekarar 2015 ya lakume tarin rayuka.

Eran Bedavid, daga Jami’ar Standford da ya jagoranci binciken ya ce alkaluman sun hada da yara miliyan 3 da ke kasa da shekara guda.

Binciken ya yi nazari ne kan tashe-tashen hankula 15,500 daga cikin kasashe 34 na nahiyar ta Afirka.