An Dakatar Da Limamin Juma'a Saboda Ya Soki Saudiyar A Moroco
Ma'aikatar dake kula da harakokin Addini ta kasar Maroco ta dakatar da wani limimin juma'a saboda ya soki siyasar Saudiya a gabashin kasar
Kafar watsa labaran jaridar AlQudusul-Arabie ta habarta cewa ma'aikatar kula da harakokin addini ta kasar Moroco ta dakatar da Abdulhamid Najari limamin juma'ar garin Berkane dake gabashin kasar saboda a khodubarsa ya soki siyasar kasar Saudiya.
A cewar ma'aikatar kula da harakokin addinin ta Moroco an dauki wannan mataki ne kan limanin saboda ya shiga fagen siyasa, tare da da'awar cewa bai kamata Limiman juma'a na kasar su dinga shiga harakokin siyasa ba.
Ma'aikatar ta ce matsayar da Limamin juma'ar ya dauka ya sabawa dokokin khodubar Juma'a da Sarkin kasar ya sanya hannu kanta.
A cikin khodubar juma'ar tasa Abdulhamid Najari ya yi kakkausar suka kan ta'addancin hukumomin masauratar saudiya kan al'ummar kasar da al'ummar kasar Yemen, tare da bayyana fatansa da kuma rokon Allah na ya gaggauta kawo karshen wannan zalinci da kuma ceto Ka'abat daga kangin masarutar Ali Sa'oud.
Gwamnatin Maroco dai nada kusanci da masarautar saudiya kuma tana goyon bayan ta'addancin da kasar saudiya ke aiwatarwa kan al'ummar kasar Yemen.