Shugaba Buhari Ya Ce Baya Jin Tsaron Zabe Na Gaskiya A Kasar.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33019-shugaba_buhari_ya_ce_baya_jin_tsaron_zabe_na_gaskiya_a_kasar.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda a halin yanzu yake ziyara a kasar China ya fadawa yan najeriya mazauna kasar ta China kan cewa ba ya jin tsoron a gudanar da zabe na gaskiya a tarayyar ta Najeriya don ta wannan hanyar ce ya kaiga matsayin da yake rike da shi.
(last modified 2018-09-03T06:29:42+00:00 )
Sep 03, 2018 06:29 UTC
  • Shugaba Buhari Ya Ce Baya Jin Tsaron Zabe Na Gaskiya A Kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda a halin yanzu yake ziyara a kasar China ya fadawa yan najeriya mazauna kasar ta China kan cewa ba ya jin tsoron a gudanar da zabe na gaskiya a tarayyar ta Najeriya don ta wannan hanyar ce ya kaiga matsayin da yake rike da shi.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya nakalto shugaban yana cewa abinda ya rage ga wadanda suka cancanci zabe shi ne su yi rigista sannan su karbi katunan zabensu don zaben wanda suke so a ranakun zabe. 

Damgane da harkokin tsaro kuma shugaban ya ce gwamnatinsa ta sami nasarori masu yawan don a halin yanzu babu wani yanke na kasar dake hannun mayakan boko haram.

A bangaren rikicin makiya da manoma kuma shugaban Buharu ya bukaci kafafen yada labaran kasar da su nemi sanin tarihin rikicin kafin su yi rubutu a kansa.

Sai kuma ga yan Najeriya wadanda suka sami tallafin karatu na gwamnatin kasar China da su yi amfani da damar da suka samu don ci gaban kansu da kuma kasarsu.

Sai kuma jakadan Najeriya a kasar China Baba Ahmed-Jidda  wanda ya gudewa shugaban kasar kan taimakon da ya bayar na kammala gida ofishin jakadncin Najeriya a birnin Bejin, sannan ya bukaci shugaban kasar ya zanda da hukumomin china don sawwakawa yan nageriya samun Visa zuwa kasar Ta China.