Angola: Mutane 17 Sun Rasa Rayukansu A Wani Mummunan Hadarin Jirigin Kasa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33053-angola_mutane_17_sun_rasa_rayukansu_a_wani_mummunan_hadarin_jirigin_kasa
Akalla mutane 17 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon wata ta ho mu gama da wasu jiragen kasa guda biyu suka yi a kasar Angola.
(last modified 2018-09-05T04:56:47+00:00 )
Sep 05, 2018 04:56 UTC
  • Angola: Mutane 17 Sun Rasa Rayukansu A Wani Mummunan Hadarin Jirigin Kasa

Akalla mutane 17 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon wata ta ho mu gama da wasu jiragen kasa guda biyu suka yi a kasar Angola.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, hadarin ya faru ne a jiya yankin Munhinu da ke ke kudancin kasar Angola, bayan da jiragen kasa guda biyu, daya na daukar kaya, daya kuma na ma'aikata masu gyaran layin dogo na wani kamfanin kasar Sin.

Mahukunta a kasar ta Angola sun ce mutane 17 sun rasa rayukansu, daga ciki kuwa har da injiniyoyin gyaran layin dogo su biyu, da kuma wani ma'aikaci dan kasar China.

Wannan dai shi ne karo na biyu da aka samu hadarin jirgin kasa irin wannan a kasar Angola, inda a cikin watan Fabrairun wanna shekara ma wani jirgin kasa dauke da fasinjoji ya fita daga kan hanyarsa, amma babu wanda ya rasa ransa, sai wasu sun samu raunuka.