Cutar Ebola Na Ci Gaba Da Kisa A Kasar D/Congo
Hukumomin jamhoriyar Congo sun sanar da mutuwar mutane da dama a lardin Butembo da ke yankin gabashin kasar sakamakon cutar Ebola.
Wannan ita ce sanarwar farko da hukumomin lardin na Butembo suka sanar na kisan da cutar Ebola ta yiwa mutanan yankin a baya-bayan nan.
Lardin Butembo da ke da yawan al'umma kusan miliyan guda, na da kan iyakar kasar da Yuganda abin da ke tsaiko ga yunkurin dakile yaduwar cutar, kamar yadda mahukuntan kasar suka tabbatar.
Rahotanni sun nunar da cewa daga watan Yulin wannan shekara kawo yanzu, mutane 85 ne suka hallaka sakamakon cutar ta Ebola a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon, yayin da wasu 39 suka kamu da ita.
Da yawa daga cikin wadanda cutar ta kama da ma wadanda suka mutu sakamakon kwayar cutar ta Ebola dai, na cikin kauyuka ne inda aka samu rahoton bullar cutar kala 20 a yankin Beni mai iyaka da kasar Ruwanda.