Mugabe Ya Amince Da Mnangagwa A Matsayin Halastaccen Shugaban Zimbabwe
(last modified Sat, 08 Sep 2018 10:31:37 GMT )
Sep 08, 2018 10:31 UTC
  • Mugabe Ya Amince Da Mnangagwa A Matsayin Halastaccen Shugaban Zimbabwe

Tsohon shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe, ya amince da Emmerson Mnangagwa a matsayin halaltaccen shugaban kasar bayan da a baya ya zarge shi da cin amana da juyin mulkin da ya kawo karshen mulkinsa na kusan shekaru 40 a kasar.

Jaridar The Herald ta kasar ta bada labarin cewa Mugaben ya bayyana hakan ne a wajen jana'izar sirikarsa inda yace ya amince da Mnangagwa din a matsayin halaltaccen shugaban kasar duk kuwa da cewa a halin yanzu dai madugun 'yan adawan kasar Nelson Chamisa bai amince da sakamakon zaben ba.

Mugabe ya ce kuskuren da aka yi a watan Nuwamba a halin yanzu dai ya wuce bayan nasarar da shugaba Mnangagwa din ya samu a zaben 30 ga watan Yulin nan, don haka yanzu muna da gwamnatin da aka kafa ta bisa kundin tsarin mulkin kasa. Don haka na amince da shugabancinsa.

Kafin hakan dai Mugaben ya ce zai zabi dan takarar jam'iyyar adawa ne don abin da ya kira kokarin kawo karshen gwamnatin mulkin soji.