An Sanya Dokar Ta Bace A Babban Birnin Harare Na Zimbabwe
(last modified Tue, 11 Sep 2018 19:08:48 GMT )
Sep 11, 2018 19:08 UTC
  • An Sanya Dokar Ta Bace A Babban Birnin Harare Na Zimbabwe

Gwamnatin kasar Zimbabwe ta sanya dokar ta bace a Harare babban birnin kasar biyo bayan billar cutar kwalara

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya habarta cewa gwamnatin kasar Zimbabwe ta sanar a yau talata da sanya dokar ta bace a Harare babban birnin kasar biyo bayar barkewar cutar kwalara da ya zuwa yanzu ta salwata rayukan mutum 20 a birnin.

Ya zuwa yanzu dai sama da mutum dubu biyu ne suka kamu da cutar ta kwalara a birnin na Harare.

Kafin hakan dai tun kwanaki goma da suka gabata, magajin garin na birnin Harare ya dauki mataken dakile cutar ta hanyar samarwa mazauna birnin tsabtaceccen ruwan sha.

A jiya Litinin Babbar daraktar  kula da harakokin kiyon lafiya na birnin Harare Clemens Dori ta yi ishara kan yadda cutar kwalarar ke kara wanzuwa a kudu maso yammacin kasar, inda ta ce ya zuwa yanzu akwai mutum 106 dake kwance a asibitin birnin na Harare sakamakon kamuwa da cutar ta kwalara.