Shugaba Muhammadu Buhari Ya Sanar Da Aniyarsa Ta Sake Tsayawa Takara
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33160-shugaba_muhammadu_buhari_ya_sanar_da_aniyarsa_ta_sake_tsayawa_takara
Kamfanin dillancin labarun Faransa ya nakalto cewa a jiya Laraba shugaba Muhammadu Buhari dan shekaru 75 ya ziyarci ofishin jam'iyyar APC mai mulki inda ya cike fom din tsayawa takara
(last modified 2018-09-13T07:42:03+00:00 )
Sep 13, 2018 07:42 UTC
  • Shugaba Muhammadu Buhari Ya Sanar Da Aniyarsa Ta Sake Tsayawa Takara

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya nakalto cewa a jiya Laraba shugaba Muhammadu Buhari dan shekaru 75 ya ziyarci ofishin jam'iyyar APC mai mulki inda ya cike fom din tsayawa takara

Muhammadu Buhari wanda tsohon shugaban kasar na soja ne, an zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2015 wanda a karon farko ya yi nasara akan shugaban da ke kan karagar mulki Goodluck Jonathan.

shugaba Buhari ya yi alkawalin fada da cin hanci da rashawa a cikin kasar da take da tattalin arziki mafi girma a nahiyar Afirka.

Sake tsayawa takarar da shugaba Buhari ya yi, ya zo ne a lokacin da kasar take fama da matsalolin tsaro wanda yake tasiri ga bunkasar tattalin arzikin kasar.