Fursunonin Siyasa Suna Cikin Mawuyacin Hali A Gidajen Kurkukun Kasar Masar
Fursunonin siyasa da ake tsare da su tun bayan rikicin siyasar kasar Masar a shekara ta 2013 suna cikin mawuyacin hali a gidajen kurkuku.
Shafin watsa labaran Arab Al-Jadid ya habarta cewa: Anwar Al-Jamawi manazarci kan harkokin siyasar kasashen Larabawa a jiya Laraba ya bayyana cewa: Mahukuntan Masar suna cin zarafin fursunonin siyasar kasar da ake tsare da su a gidajen kurkuku tun bayan rikicin siyasar shekara ta 2013 bayan da sojoji suka kifar da zababbiyar gwamnatin Muhammad Morsi na kungiyar Ihwanul-Muslimin ta kasar.
Al-Jamawi ya kara da cewa: Mahukuntan Masar karkashin shugabancin Abdul-Fatah Al-Sisi suna ci gaba da musgunawa al'ummar kasar musamman 'yan adawars siyasa, lauyoyin da basu tare da gwamnati da sauransu, kamar yadda suka cika gidajen kurkuku da 'yan adawar siyasa tare da cin zarafinsu.