'yan Boko Haram Sun Kai Wa Sojojin Najeriya Hari
Majiyar tsaron Najeriya ta sanar da kai harin mayakan 'yan ta'adda na boko haram kan sansanin sojoji na garin Damasak na jahar Borno dake shiyar arewa maso gabashin kasar
A cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Alhamis Rundunar Sojojin Najeriya ta Maiduguri babban birnin jahar Borno dake shiyar arewa maso gabashin kasar ta sanar da cewa a daren jiya laraba Sojoji sun dakile wani hari da mayakar kungiyar Boko haram suka kai a sansanin soja na garin Damasak dake kan iyakar kasar da jamhoriyar Nijer.
Sanarwar ta ce Sojojin sun samu nasarar hallakar mayakan 'yan ta'addar na boko haram guda goma a yayin fafatawar.
Wannan hari dai shi ne irinsa na biyu da mayakan boko haram din suka kaiwa Sojojin Najeriya a jahar Borno kasa da mako guda kacal
Ko a karshen makon jiya ma 'yan Boko Haram din sun kai wa sojojin hari a garin Gudumbali a karamar hukumar Guzumala a jihar ta Borno, inda Boko Haram ta ce ta kashe sojoji da dama ta kuma kwaci makamai da motocin yaki.
To sai dai rundunar sojan Najeriya ta musanta ikirarin, inda ta fitar da wata sanarwa tana cewa sojojin da suka tarwatse sakamakon harin da aka kai musu sun sake haduwa wajen daya, sun kwace garin kuma ba a samu asarar rayuka ba.