An Kafa Sabuwar Gwamnati A Kasar Sudan
Mataimakin Shugaban kasar Sudan ya sanar da kafa sabuwar gwamnatin hadin kan kasa mai kumshe da ministoci 21 da mashawartan ministoci 27 a kasar
Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar China ya nakalto mataimakin shugaban kasar Sudan Faisal Hassan Ibrahim ya ce a sabuwar gwamnatin an rage yawan ministoci daga 31 zuwa 21, kuma jam'iya mai milki nada ministoci uku ne kacal da suka hada da ministan cikin gida, da ministan tattalin arziki gami da minstan ruwa.
A 'yan kawanakin da suka gabata ne Shugaba Albashir na kasar Sudan ya rusa majalisar zartarwar kasar bisa jagorancin firaminista Bakri Hassan Saleh, sannan kuma ya nada Mu'utaz Moussa a matsayin sabon firaminstan kasar.
Shugaba Al-Bashir ya dauki wannan matakin ne domin rage matsalar tattalin arzikin da kasar ke fada da shi.
Kafin daukan wannan mataki dai, Shugaban kasar ta Sudan ya rage yawan ma'aikatan Diplomasiyar kasar a kasashen waje.