Amurka Ta Fara Kai Farmaki Kan Kungiyar Ashabab A Somaliya
(last modified Fri, 14 Sep 2018 13:00:38 GMT )
Sep 14, 2018 13:00 UTC
  • Amurka Ta Fara Kai Farmaki Kan Kungiyar Ashabab A Somaliya

Rundunar sojojin kasar Amurka ta sanar da samun nasarar kashe wasu mayakan kungiyar Al-shabaab yayin musayar wuta tsakanin dakarunta da Sojojin Somaliya da kuma mayakan 'yan ta'addan.

Sanarwar ta kara da cewar an fara harin na hadin gwiwa ne tun cikin mako da ya gabata, a kauyen Mubaraak da ke yammacin birnin Mogadishu.

Kasar Amurka dai na goyon bayan gwamnatin Somaliya a kan yaki da 'yan ta'dda, wadanda har yanzu suke rike da wasu yankunan kasar.

A 'yan kwanakinnan dai mayakan na kungiyar Al-shabaab sun zafafa kai hare-haren kan fararen hula a kasar ta Somaliya.

Kimanin Shekaru 25 kenan da kasar Somaliyan ke fuskantar hare-haren ta'addanci na kungiyar Ashabab.kafin hakan dai, Kungiyar ta Ashabab na  mamaye da wani bangare a tsakiya da kuma kudancin kasar, saidai a 'yan shekarun nan, Dakarun tsaron kasar tare da taimakon Dakarun kasashen Afirka sun kwace mafi yawan gariruwan.